Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Lantarki Ta Dauke A Ukraine


Russia - Ukraine
Russia - Ukraine

A ranar Lahadi ne aka dauke wutar lantarki cikin gaggawa a sassan kasar Ukraine, kwana guda bayan da Rasha ta yi ruwan hare-hare da jirage marasa matuki guda 100 da makamai masu linzami kan cibiyoyin samar da makamashin kasar.

WASHINGTON, D. C. - Haka kuma Rasha ta yi ikirarin kwace yankuna a gabashin yankin Donestsk na kasar ta Ukraine.

A kalla mutane 19 ne suka ji rauni a gagarumin hare-haren da ta kai a ranar Asabar da ta wuce.

Rashin wadatacciyar kariya ga sararin samaniyar ta, da damar gudanar da gyare-gyare kan cibiyoyin makamashin Ukraine a 'yan makonnin nan, yasa a kan dole Kyiv ta rage karfin wutar lantarki a fadin kasar, domin cike gurbin karancin wutar lantarkin a yanayi na bazara da ake fama da zafin rana da ma na tsananin sanyi a lokutan hunturu.

A ranar Lahadin ne dai Rasha ta yi ikirarin karbe iko da kauyen Umanske a yankin da ta dan mamaya na Donetsk, yayin da ta ke kara kutsa kai a yankunan Sumy da Chernihiv na arewacin Ukraine.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG