A jiya Juma’a a wani taron da hukumar ta saba yi a helkwatarta a Geneva, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce a shekarar da ta gabata a ranar Asabar, adadin kamuwa da cutar bai kai guda dari ba kana babu wanda ya mutu da cutar a wajen China.
A cikin makon nan, mutane da suka kamu da cutar sun haura miliyan dari kana mace mace ya tasar ma miliyan guda da dubu dari biyu. Tedros ya fada cewa, a waccan lokaci ya gargadi duniya cewa akwai damar dakile yaduwar cutar. Ya kara da cewa wasu kasashe sun dauki shawarwarin wasu kuma sun ki dauka.
Tedros ya ce allurar rigakafi da aka samu a yanzu ta sake baiwa duniya wata dama ta kawo karshen wannan annoba, kana ya ce bai kamaci a yi warwason rigakafin ba, a raba ta daidai wa-deda tsakanin kasashe masu arziki da talakawa.
Tedros ya kalubalanci abin da ya kira da masu kishin samar da rigakafi, yana nuni da batun boye rigakafin da wasu manyan kasashen duniya ke yi yanzu, yayin da kasashe matalauta ke zaman jira allurar.