Fadar shugaban Amurka ta White House ta bayyana tababa akan wani rahotan da ke hasashen cewa, adadin wadanda ke mutuwa a kullun sanadiyar COVID-19 a Amurka zai ninka nan da 1 ga watan Yuni.
Mai Magana da yawun fadar ta White House Judd Deere, a jiya litinin, ya bayyana shakku kan rahoton cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa CDC, wanda ta yi hasashen cewa, za’a samu karuwar sababbin wadanda kamuwa da cutar 200,000 a rana, daga 25,000 da ake samu yanzu.
Wannan bayanin ya fito ne daga jerin bayanai da hukumar bada agajin gaggawa take badawa, wanda jaridar New Times ta wallafa a jiya litinin.
A bayani da ya fitar jiya litinin Deere ya fadi cewa, wannan ba bayani bane da ya fito daga fadar White House, ko kwamitin coronavirus, kuma ba bayani bane da ya bi ta hannun masu fada a ji. Ya ce, baya daga kundin bayanan kasar ko wanda kwamitin ya amince da shi.
Jami’in na White House ya jaddada cewa lafiyar Amurkawa shine abu mafi muhimmanci ga shugaba Trump, kuma suna ci gaba da bibiyar yadda jihohi ke tafi da lamarin.
Facebook Forum