Kasar China ta zargi Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da abin da ta kira, “yada kalamai masu hadari da kararerayi” game da inda cutar corona, wadda ta game duniya, ta samo asali.
Kwana daya gabanin nan, babban jami’in diflomasiyyar Amurka din, ya ce, “akwai kwakkwarar shaidar” cewa cutar ta samo asali ne daga wani dakin binciken sinadarai da ke Wuhan, kasar China, ba wata kasuwar da ke daura da wurin ba.
Amma kafar yada labaran gwamnatin China ta CCTV, ta caccaki abin da ta kira “kame-kame na fitar hankali” da Pompeo ya yi, tana mai ikirarin cewa ba kirkiro cutar aka yi ba.
A wani shirin gidan talabijin din ABC mai suna “This Week” Pompeo ya ce, “Ku tuna fa, China na da tarihin yada cuta a duniya, kuma suna da tarihin amfani da dakunan bincike marasa inganci."
Ya kara da cewa, "wannan ba shi ne karon farko da duniya ta fuskanci yaduwar wata cuta sanadiyyar rashin kwarewa a dakunan binciken China ba.”
Facebook Forum