Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ouattara Yayi Kiran A kawo karshen Cin Zarafin


Wani mutun na kenan ke nuna wani shagon da ya kone kusa da unguwar Williamsville bayan wani fada tsakanin jami’an tsaron Ivory Coast da mayakan da ke goyon bayan Ouattara a birnin Abidjan.
Wani mutun na kenan ke nuna wani shagon da ya kone kusa da unguwar Williamsville bayan wani fada tsakanin jami’an tsaron Ivory Coast da mayakan da ke goyon bayan Ouattara a birnin Abidjan.

Alassane Ouattara, mutumin da kasa da kasa tace shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a Ivory Coast, yayi kiran da’a kawo karshen tarzomar da cin zarafin bakin haure.

Alassane Ouattara, mutumin da kasa da kasa tace shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a Ivory Coast, yayi kiran da’a kawo karshen tarzoma da cin zarafin bakin haure.

A jiya Laraba Mr Ouattara yace ana maraba da baki su zauna a Ivory Coast. Yayi kira ga dukkan yan kasar da su gina kasar da zata yiwa kowa kara. Mr Ouattara yayi wannan furucin ne daga otel din da yake zaune inda sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke gadi.

Kungiyar dake hankoron kare hakkin jama’a ta Human Rights watch ta zargi sojojin dake biyaya ga shugaba Laurent Gbagbo da laifin auna yan gudun hijira daga Mali da Burkina Faso da Nigeria da kuma Niger suna lakada musu duka, a wasu lokutan ma su konasu da ransu.

Haka kuma kungiyar Human Rights Watch tace laifuffukan da sojojin dake biyaya ga Gbagbo suka aikata cikin watani uku da suka shige, sun hada harda fyade da karkashe mutane, laifuffukan da za’a iya dauka a zaman laifuffukan yaki.

Ana kuma ci gaba da fafatawa a Abidjan. Shedun gani da ido sun bada rahoton cewa anyi mummunar fafatawa a birnin Dueloue kusa da kan iyakar kasar da Liberia.

Rundunar ‘yan tawayenda ake kira New Forces, wadanda suke goyon bayan Ouattara suna kara dannawa kudanci cikin yankin dake hannun sojojin Gbagbo. Kungiyar New Forces tace cikin ‘yan makonin da suka shige ta kwace birane hudu na yammacin kasar daga hannun sojojin shugaba Gbagbo.

XS
SM
MD
LG