Zaman kashe wando abu ne da ya kusan zama ruwan dare a Najeriya musamman tsakanin matasan kasar, inda a lokuta da dama lamarin ke kai su ga shiga yanayin da ke da hatsarin gaske, amma yanzu masu ruwa da tsaki daga bangarorin Najeriya dabam-daban sun fara jajircewa wajen zakulo hanyoyin kawo karshen wannan matsalar.
A daidai wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar matsi ta fuskar tattalin arziki, abu mafi dacewa shi ne horar da matasa yin sana’o’i dabam-daban musamman domin su zama masu dogaro da kai da kuma yin gogayya da sauran ‘yan uwan su a fadin duniya.
A wurin tsaron bada horon da aka shirya na makonni biyu, dan majalisar wakilai a Najeriya, Honarabul Kabir Ibrahim Tukura mai wakiltar mazabar Zuru/Fakai/Danko-Wasagu/Sakaba, ya ce suna so ne su kawo wani salo na dabam na horar da matasa, ba basu babura ko keken dinki ba wanda wasunsu ke saidawa.
Wadanda suka ci gajiyar shirin sun yi bayani akan damar da suka samu tare da bayyana farin cikinsu matuka.
A cikin kwararrun da suka koyar da matasan, Umar Navid Muhammad, ya ce gaskiya an samu ci gaba sosai, kuma wannan zai bai wa matasa damar gogayya da sauran ‘yan uwansu matasa a duk fadin duniya.
A wani bangare kuwa, ma’aikatan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, na kara himma wajen tabbatar da samar da gudunmowa ga tattalin arzikin Najeriya ta fuskar yin bita don inganta tsarin shigar da fasahar zamani da kirkire-kirkire cikin kasuwanci, saboda a inganta yanayin kasuwanci musamman ga masu basirar kirkire-kirkiren fasahohin zamani.
Ga cikakken rahoton Madina Dauda ta sauti: