Ministan na tafe ne da wani sakon da yace Shugaba Patrice Talon ya umurce shi ya damka wa Janar Abdourahamane Tiani a matsayin tayin sulhu.
Makasudin wannan taron, da ya hada jami’an China da Nijar da na Benin a tsawon wuni 2 a birnin Yamai, shine zakulo hanyoyin da zasu bada damar karfafa matakan dorewar aiyukan bututun man da ta hanyarsa Nijar ta fara fitar da danyen manta zuwa kasuwannin duniya a ranar 19 ga watan Mayun 2024 daga tashar jirgin ruwan Seme a jamhuriyar Benin.
Yayin zantawa da manema labarai, Ministan Ruwa da Ma’adanan Jamhuriyar Benin, Samou Seidou Adambi, Adambi yace taron ya gudana cikin yanayin fahimta.
Wannan haduwa an yita ne a wani lokacin da hukumomin Nijar da na Benin ke yi wa juna kallon hadarin kaji, sabanin da ya biyo bayan takunkumin CEDEAO mai nasaba da juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Zancen nan da ake ba shiga ba fita ta kan iyakokin kasashen 2.
Yayinda Nijar ke zargin Benin da bai wa sojojin Faransa damar kafa sansani da zummar kitsa wata ta’asa, ita kuwa Benin ta ce zargi ne marasa tushe.
A haka ne Ministan Ruwa da Ma’adinan Benin ya bukaci ya gana da Janar Tiani a fadarsa da nufin isar da sakon Shugaba Patrice Talon wanda ke kunshe da tayin sulhu a cewarsa.
Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren mahukuntan Nijar a game da bayanan na Ministan, yayin da kungiyoyin kare hakkin jama’a suka fara bayyana matsayinsu a kan wannan dambarwar.
Jigo a kungiyar MPCR Ibrahim Namewa ya yaba da matakin na Shugaban Majalisar CNSP.
Sai dai Shugaban kungiyar MOJEN, Siraji Issa, na ganin rashin dacewar wannan mataki.
Yanayin tabarbarewar dangantaka a tsakanin Nijar da Benin na kara fitowa fili a wani lokacin da sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ke ziyarar kasashen Burkina Faso da Mali a wannan Alhamis wanda aka bayyana cewa ko baya ga batun karfafa hulda a tsakanin kasarsa da wadanan kasashe rangadin nasa yunkuri ne na bikon kasashen AES wadanda a karshen watan Janairun 2024 suka bada sanarwar ficewa daga kungiyar ECOWAS sakamakon zarginta da kaucewa ainihin manufofin kafata.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna