Tawagar masu tsaron shugaba Buhari da wasu ma’aikatan ofishin magoya bayansa sun kai ziyara ofishin muryar Amurka a Abuja inda suka yi korafin gwamnati bata waiwaye su ba tun bayan rantsuwar shugaba Muhammadu Buhari ta kama aiki.
Jami’an maza da mata sunce sunyi tsammanin samun aiki ko yi masu wani abu da za’a yaba masu tunda gwaninsu ya lashe zabe bayan karo hudu yana tsayawa takara.
Ma’aikatan da suka ki ficewa daga ofishin kamfe na shugaba Buhari dake dab da kamfanin fetur na NNPC sunce suna da kyakkywar fata Buhari zai share masu hawaye a yanayin da suka ce sun shiga na halin kaka nikayi wanda ya hada da barazanar fatattakar su daga ofishin kamfe din bayan umurnin da aka bada na kwance nau’rorin sanyaya daki dake ofishin.
Kasim Abdullahi Hassan ya kasance daya daga cikin masu tallafawa shugaba Buhari wajan lamurran tsaro a zamanin kamfe ya bayyana cewa dubu ashirin ake basu a matsayin alawus wanda rabon da aba su tun watan biyu daya gabata, kuma kawo yanzu babu abinda ya shiga hannunsu, shiyasa suke tsoron mawuyacin halin da hakan zai iya jefa su.
A mayar da martanin tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Nasiru Adamu Elhikaya yayi masa cewar aikin kamfe ya wuce mai yasa ya tada wannan Magana sai ya ce harkar siyasa kowa yana shiga ne domin bada gudummuwar sa saboda idan aka samu nasara, suma wadanda suka taka rawar gani a tafi dasu wajan cin moriyar nasarar da aka samu.
Kasim ya kara da cewa sun dade tare da shugaba Buhari tun shekarar 2003, har zuwa shekarar da ya sami nasarar lashe zabe suna mara masa baya, dan haka sun yi tunanin cewa tunda an sami nasara yanzu lokacine da yakamata gwamnati ta tuna dasu.
Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.