Masu taya alkali yanke hukuncin Amurka sun sami tsohon shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya John Ashe da laifi bisa zargin karbar cin hancin Dalar Amurka miliyan daya don ciyar da bukatar wani dan kasuwar kasar Sin.
Mista Ashe ne tsohon jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Antigua da Barbuda tun daga shekarar 2004 har zuwa lokacin da aka zabe shi shugaban zauren majalisar a shekarar 2013.
Wannan tabbatar da laifin nasa ya biyo bayan kamun da aka yi masa ne a wata unguwa dake birnin New York.
Yanke hukuncin laifin ya shafi attajirin nan mazaunin Macau mai huldar bunkasa muhalli mai suna Ng Lap Seng da wasu suka sani da David Ng, da kuma wasu mutane guda uku.