Jagoran ‘yan hamayyar kasar Uganda, Kizza Besigye yace an hana shi shiga jirgin sama da zai taso daga kasar Kenya zuwa Uganda, kwana guda kafin bikin rantsar da shugaba Yoweri Museveni zagaye na hudu a matsayin shugaban kasa.
A yau laraba, Besigye yace wani jami’in kamfanin jirgin saman Kenya Airways ya shaiada masa cewar Gwamnatin Uganada tacae ba zata baiwa jirgin saman fasinja iznin sauka ba idan har aka bari Besigye ya shiga jirgin saman. Amma jami’an Gwamnatin Uganda sun musanta wannan zargi, suka ce babu hannun Gwamnatin Uganda a harkokin jigilar jiragen saman fasinja.
Besigye, yaje kasar Kenya ne domin neman magani inda aka kwantar dashi a wani asibitin birnin Nairobi inda ake kula da ciwon aka ji masa a dalilin gwabzawar da suka yi da ‘yan sanda a lokacin kokarta jagorancin yin zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Uganda. Mutane akalla takwas ne suka halaka, sannan sama da mutane metan da hamsin suka jikkata.