Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Gabashin Afrika Na Cigaba Da Lalubo Hanyoyin Kawo Karshen Rikici A Gabashin Congo


Yan tawayen Congo
Yan tawayen Congo

  kasashen gabashin Afrika sun sake yin wani hubbasa kan batun samun zaman lafiya a gabashin Congo, duk da dai ana ganin bukatar tasu na da rauni.

kasashen gabashin Afrika sun sake yin wani hubbasa kan batun samun zaman lafiya a gabashin Congo, duk da dai har yanzu bukatar tasu na da rauni, biyo bayan wani babban taron yankin da ya gaza samun halartar shugaban kasar ta Congo, da barin zauren taron cikin sauri da takwaran shi na Rwanda yayi.

Wata sanarwar bayan taro da aka fitar a karshen taron da aka gudanar a asirce na al’ummar kasashen gabashin Afrika a Arusha ta Tanzaniya, ta sanar da jaddada bukatar hada karfi da karfe domin samar da zaman lafiya mai dorewa a gabashin Congo.

Rikici ya sake barkewa a wani yanki mafi ganin bala’in tashin hankali a duniya dake gabashin Congo, inda gwamnatin Congon ta zargi kungiyar yan tawaye ta M23 dake kisan kiyashin kabilu da Rwanda ke marawa baya, a yankunan da ke da arzikin albarkatun karkashin kasa na kusa da kan iyaka da Rwanda.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya fice daga taron da aka gudanar jim kadan da kammala taron da aka gudanar a Arusha. Hakazalika, ba wani bayani a hukumance da aka bayar dangane da rashin halartar shugaban Congo Felix Tshisekedi a babban taron.

Congo na zargin Rwanda da hannu a laifuffukan yaki a yankin gabashi, hakazalika kwararru daga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya duk sun zarge ta da bayar da tallafin soji ga kungiyar yan tawayen ta M23. Rwanda ta karyata zargin, to amma a watan Fabrariru ta amince cewa, tana da dakaru da makamai masu linzami a gabashin Congo, domin inganta tsaron ta, da nuna cewa tana kara habaka karfin dakarun Congo dake kusa da kan iyaka. Kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya sun kiyasta cewa, akwai akalla dakarun Rwanda har 4,000 a Congo.

Wata yarjejeniyar zaman lafiya da kasashen Amurka da Angola suka samar a watan Yuli ta rage fadan da ake yi tsakanin dakarun Rwanda da na Congo, to amma fada na cigaba tsakanin M23 da sauran yan tada kayar baya.

Sauran shugabannin da su ka halarcin taron sun hada da shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu, Samia Suluhu Hassan ta Tanzania, William Ruto na Kenya, Yoweri Museveni na Uganda da Hassan Sheik Mohamud na Somalia. Mataimakin shugaban kasar Burundi ne ya wakilci shugaban kasar a taron.

An zabi Ruto a matsayin sabon shugaban babban taron na kasashen yankin gabashin Afrika EAC inda ya gaji shugaba Kiir.

Da yake Magana, sabon shugaban yace, dole ne sum aida hankali wajen kara jajircewa wajen shiga a dama da su a duk wata harka da cigaban su, kamar inganta huldar kasuwanci a tsakanin su domin samar da aiyukan yi da bunkasa tattalin arzikin su.

Ruto ya kuma yi kira ga mambobin kasashen da su jajirce wajen bayar da gudummuwar da amince akai, akan lokaci domin samun dorewar aikace aikacen kungiyar kasashen.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG