Tun farko dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasan da aka gudanar a jihar Neja, ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.
A wani taron manema labarai da Shugaban jam'iyyar ta PDP a jihar Nejan Barista Tanko Beji ya yi kira ga al'umma da su fito su yi zaben sannan ya bukaci hukumar ta INEC ta tabbatar ta yi tanadin jami'an tsaro a dukkanin rumfunan zabe dake fadin jihar Neja.
Jam'iyyar APC da ta nuna gamsuwa da yadda zaben ya gudana a baya amma tace rashin yawon takardun kudi a hannun jama'a ya kawo nakasu sosai a cewar shugaban APC a jihar Nejan Hon.Halliru Zakari jikantoro.
Hukumar zaben dai ta ce tana nan akan bakanta na tabbatar da yi wa kowa adalci a zaben kamar yadda Kwamishinan Hukumar zaben mai kula da Jihar Nejan Alh.Yusha'u Garki ya fada.
A yanzu dai hankali ya karkata zuwa ranar Asabar Mai zuwa yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da fadakarwa akan muhimmancin yin zaben lafiya.