Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Iran Sun Kona Tutocin Faransa A Birnin Tehran


Zanga-zangar Iran
Zanga-zangar Iran

Masu goyon bayan tsarin Jamhuriyar Musuluncin Iran sun kona tutocin Faransa a wajen ofishin jakadancin Faransar da ke birnin Tehran, inda suka yi zanga-zangar nuna adawa da wani zanen barkwanci da mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta wallafa kan shugaban addinin Iran.

An wallafa zanen ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran, wadda aka kwashe wata na hudu ana yi. Masu zanga zangar dai na neman a kawar jamhuriyar Musuluncin Iran.

Zanga-zangar da aka yi ranar Lahadi a wajen ofishin jakadancin Faransa na zuwa ne bayan yukurin da mahukuntan Iran suka yi a baya na neman magoya baya da zasu kalubalanci masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin.

Daruruwan masu zanga-zangar da suka hada da dalibai sun yi ta kiran “Mutuwa ga Faransa” sun kuma zargi shugaban Faransa Emmanuel Macron da cin mutuncin Iran, yayin da suka yi kira ga Faransar da ta daina nuna kiyayya ga Tehran.

Gidan talabijin din Iran ya ce wasu malaman addini sun gudanar da shigen irin wannan zanga-zangar a birnin Qom, inda ke zaman cibiyar koyar da ilimin addini a Iran.

A ranar Lahadi, kakakin majalisar dokokin Iran Mohammad Bagher Qalibaf, ya alakanta zane-zanen mujallar ta Faransa da abinda jami'ai suka yi ta zargin cewa kasashen yammacin duniya na kitsa yada tarzoma a Iran.

XS
SM
MD
LG