Wasu maharba guda biyu dake taimakawa wurin yaki da 'yan Boko Haram sun share sama da watanni biyu a tsare cikin hali na kunci da azaba a hannun sojojin Najeriya.
Bayan an gana masu azaba ta kin kari aka kuma mikasu ga cibiyar bincike ta manyan laifuka ta 'yansandan Najeriya.
Yahaya da Inusa wadanda aka sakaye sunayensu saboda dalilai na tsaro sun fada cewa an tsaresu ne sakamakon tuhumarsu da ake yi na kisan wasu 'yan Boko Haram guda biyu da aka tsare a ofishinsu.
Jama'ar garin Mildu cikin karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa suka kashe 'yan Boko Haram din a wani yanayi mai kama da ramuwar gayya lokacin da suka samu labarin cewa 'yan Boko Haram din na tsare a ofishin 'yan bangan.
'Yan bangan sun shaidawa Muryar Amurka abun da ya faru bayan da aka sakosu. Sun ce sun kama 'yan Boko Haram din biyu amma 'yan garin Mildu suka yi turuwa suka kashe su a matsayin ramuwar barnan da 'yan Boko Haram din suka yi masu.
Saboda mutuwar 'yan Boko Haram din aka kamasu ana zarginsu da kashesu. Sun yi wata daya a Mubi a hannun sojoji kafin a turasu zuwa Yola hannun 'yansanda. A cewarsu babu irin azbar da ba sojoji basu nuna masu ba a Mubi. Haka ma bata sake zani ba yayin da ak kaisu Yola har zuwa lokacin da aka sakesu jiya.
Ga cikakken rahoton Sanusi Adamu.