Mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutane 21 a wani hari da suka kai kusa da Chibok, kamar yadda majiyoyi suka shaidawa kafofin yada labarai jiya jumma'a.
Rahotanni sun ce 'yan tawayen suna gudu ne daga farmakin da dakarun gwanati suke kai musu a dajin Sambisa,a kokarin tserewan ne suka kai hari kan akalla kauyuka biyu a jihar Barno.
A cikin watan Afrilun bara ne duniya duka ta sami labarin Chibok sa'ilinda 'yan bindigar suka sace 'yan mata 'yan makaranta su fiyeda metan.
Haka daga yankin Hong a jihar Adamawa ma mun sami labarin cewa mayakan sakan sun kai hari kan wasu kauyuka akalla biyu, inda suka halaka mutane akalla 30 a kauyukan Gaya- da kuma Zang, kamar yadda wani maharbi wanda ya ga harin ya shaidawa wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz.
Maharbin yace 'yan binidgar sun je kauyukan ne cikin motocin Hilux hudu, da dawaki uku, da kuma babura kamar ashirin. Suka saci abinci har da katifun kwana da kuma cokula.
Daga Gaya-Sa suka tafi Zang, inda suka kona wasu gidaje, suka ci gaba da barna, har sai da maharba suka taka musu birki.Daga bisani suka gudu.
Da aka tambayeshi ko jami'an tsaro sun kai musu doki, maharbin yace, dukkansu an jibge su ne a Hong, kuma da aka tuntube su ta woyar tarho suka ce, basa aiki cikin dare.
Ga karin bayani.