Mutanen da suka sace Bajamushen sun zo ne bisa kan babura suka yi dirar mikiya akan dan kasar Jamus din gaf da fitowarsa ta zuwa aiki.
Dan Jamus din shugaban wata makarantar koyas da sana'o'i ce mallakar gwamnatin jihar Adamawa.
Mazauna garin sun ce wasu 'yanbindiga ne suka zo su biyar. Sun kwana a bayan gidansa ne akan dutse domin an samu mayafinsu. Mutum uku akan babur daya biyu kuma akan daya. Bajamushen ya fito da motarsa da safe domin dansandansa an yi masa rasuwa ya tafi gida. Da ya fito bai yi wata tafiya mai nisa ba sai suka tsareshi suka nuna masa bindiga sai ya tsaya kana suka zareshi daga motar suka sashi a babur mai mutum biyu. Sun sashi a tsakiya ne.
Bayan lamarin ya faru jami'an tsaro sun bi bayan 'yanbindigan domin farautosu. Rundunar 'yansandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kungiyar maharba da 'yan sintiri suna taimakawa wajen kubuto da baturen.
'Yan bangan Hong da suka taimaka wurin tare 'yanbindigan sun yi asarar mutum biyu wadanda 'yanbindigar suka harbe har lahira suka kuma raunata daya.
Mutanen Gombi suna cikin bakin ciki domin Bajamushen yana taimaka masu. Har masallaci yana ginawa mutanen garin.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.