Kwamitin Shari'a na Majalisar Wakilan Amurka ya rubuta takardar umurnin gurfana ga wasu tsoffin manyan hadiman fadar Shugaban Amurka ta White House, bayan da tsohon babban lauyan Fadar White House, Don McGahn ya ki bin umurnin takardar gayyata da majalisar ta tura masa, don bada shaida kan ko Shugaban Amurka Donald Trump ya karya doka ko a'a.
Shugaban kwamitin, dan jam’iyyar Dimokarat Jerrold Nadler, ya ce kwamitin na so ya ji daga bakin tsohuwar darektar sadarwa Hope Hicks, da shugabar ma'aikatan McGahn, wato Annie Donaldson.
An umurce su da su samar da takardun bayanai, kuma an kira su da su bayyana a gaban 'yan majalisar Wakilai zuwa watan gobe.
Dab da yin murabus dinta a watan Maris na 2018, Hicks ta shaida wa kwamitin Majalisar Wakilai kan bayanan sirri cewa, a wasu lokutan ta kan shara, abin da ta kira, "kayar da ba ta cutarwar ba" saboda Trump.
Facebook Forum