Mutumin da ya kafa mashahurin kamfanin sadarwan nan na kasar China da ake kira Huawei, ya yi watsi da matsayar da Amurka ta dauka na muzantawa kamfanin bisa zargin cewa, yana barazana ga tsaron kasar.
A wasu jerin hirarraki da aka yi da shi da wasu kafafen yada labaran cikin gida a jiya Talata, Ren Zhengfei ya ce matakin da gwamnatin shugaba Trump ta dauka ya raina kwarewar da kamfanin ke da shi na ci gaba da ayyuka da kera sabbin wayoyin salula da ingancinsu da ya kai karfin 5G.
Umurnin da shugaba Trump ya bayar a makon da ya gabata, zai iya kawo cikas ga fannin aikawa da kuma sarrafa wasu manhajoji a wayar ta Huawei a nan gaba, lamarin da ka iya shafar bunkasar kamfanin a duk fadin duniya, da kuma yunkurin da yake yi na tserewa kamfanin Samsung na kasar Korea ta Kudu, wanda shi ne kamfani mafi girma a duniya da ke kera wayar salula.
A jiya Litinin, kamfanin Google ya bayyana cewa zai takaita damar da yake ba kamfanin na Huawei na shiga sahun wayoyin kirar Android.