Sanatoci 77 wadanda ke aiki a Majalisar dattawa tun daga 1999 zuwa 2023, da a yanzu suke jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Sanata Bashir Lado ne suka yi wannan alkawalin a yayin wata ganawa ta musamman da suka yi da zababbun wadanda uwar jam'iyya ta ce su ake so su jagoranci Majalisar Dokokin kasar, wato Sanata Godswill Akpabio daga shiyar Kudu masa Kudu da Sanata Barau Jibrin daga shiyar Arewa maso yamma.
Sanata Mas'ud Eljibrin Doguwa, yana cikin tsofaffin Sanatocin da suka halarci taron kuma yayi karin haske, yana mai cewa a yanzu jam'iyyar APC da ke kokarin zabar shugabannin Majalisar Dokokin kasa ana samun rikici, a saboda haka ne tsofaffin Sanatocin jam'iyyar suka kira wannan taro domin su ja hankali kan cewa jam'iyya ita ce gaba da kowa, in akwai kuskuren da jam'iyya ta yi, bai kamata a ba ta kunya ba.
Eljibrin ya kuma ce kamata ya yi su tsofaffin Sanatoci su zo su tabbatar an gyara kurakuran.
Eljibrin ya ce ba daidai ba ne idan za a zabi shugabannin Majalisa shugaban kasa ya sa baki har a bayyana sunayen wadanda ake so a fili karara, amma akan kai 'yan majalisa wani wuri a yi masu bita, sannan a bayyana abinda uwar jam'iyya ta ke so a boye.
Eljibrin ya ce dole ne tsofaffin 'yan majalisa su zo su bayyana irin tasu basirar da bajinta domin kar jam'iyya ta samu nakaso.
Amma Sanata Ahmed Aliyu Wadada, ya ce su daga bangaren adawa sun zo taron ne domin wani kwakwaran dalili, wanda ya ce harka ta Majalisa magana ce ta Najeriya ba domin wani mutum daya ba.
Wadada ya ce duk wani abu da za a yi a irin wannan hadaka, ba zai hana Majalisa yin aikinta ba.
Ya kara da cewa ba yadda za a yi a yi zaben shugabanni ba tare da an ba shiyar Arewa ta tsakiya ba, saboda haka a shirye suke su tabattar an ba shiyar Arewa ta tsakiya mukamai, wacce ta bada kuri'u 1,700,000 a zaben shugaban kasa.
Shi ma tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai Babangida Saidu Nguroje, ya ce yana goyon bayan wannan yunkuri.
Nguroje ya ce ana so a ga irin wannan hadaka a siyasar kasar, saboda dole ne duk abinda za a yi a yi shi da tuntuba. Ya kara da cewa, hadaka tsakanin tsofaffin 'yan Majalisa da sabbi alama ce mai kyau, kuma hakan zai hana 'yan jam'iyya zama kara zube ba tare da masu nuna masu hanyar gyara ba.
Manazarta a fannin siyasa dai na ganin irin wannan hadaka da ke faruwa barkatai na nuni da cewa an samu rarrabuwar kawuna a cuku-cukun zaben shugabannin Majalisar Dokokin kasar.
Saurari rahoton cikin sauti: