Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ya ga rahoton wasu bayanan sirri da suka nuna cewa cutar COVID-19 a wani dakin bincike aka kirkireta a yankin Wuhan na kasar China.
A lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi a Fadar White House a jiya Alhamis, shin me yake ba shi kwarin gwiwar cewa rahoton na da sahihanci, sai Shugaba Trump ya ce, “ba a yarda in yi bayani kan wannan al’amari ba.”
Sai dai Trump ya ce akwai misalai da dama, amma ba wai an fayyace bayanan sirrin ba ne, yana mai cewa za a tsaya a ga inda rana za ta fadi.
Yayin kuma da aka tambaye shi shin zai nemi a gudanar da bincike a Cibiyar Gudanar da bincike kan kwayoyin cututtuka da ke Wuhan, sai Shugaba Trump ya ce a halin da ake ciki, China ba ta nuna wata alama ta yin rufa-rufa ba, amma ya san cewa mai yiwuwa Chinar ta gaza dakile yaduwar cutar ne ko kuma da gangan ta bari cutar ta yadu.
Gabanin a yi hakan dai, ofishin daraktan tattara bayanan sirri a Amurka, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce, hukumomin tattara bayanan sirrin kasar, sun yi ittifakin cewa cutar COVID-19 ba bil adama ba ne ya kirkireta.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, hukumomin na bincike kan bayanan sirri domin tantance ko cutar daga dabbobi ta samo asali ko kuma bisa wani kuskure ne da ya auku a dakin gudanar da bincike na Wuhan.
Facebook Forum