Ranar litinin da ta gabata ne wata kotun majistire da ke birnin Legas ta aika da wasu matasa su uku, Ebuka Anosike mai shekaru ashirin, Quadri Yekini mai shekaru 23, da Moses Osagie shima shekarun sa 23 gidan yari bisa zargin su da yi wa wata yarinya 'yar shekaru 15, da ba'a fadi sunanta ba fyade.
Wadanda ake tuhuma da aikata lafin tsakanin watan tara zuwa watan goma na wannan shekarar, an cafke su ne ranar 11 ga wannan watan da muke ciki, kuma jami'an tsaron 'yan sanda na tuhumar su da aikata laifuka da suka hada da cin zarafi, fyade da hada kai wajan aikata muggan laifuka.
A cewar jami'in tsaro mai gabatar da kara Sufeta Tony Idibe, matasan na zama ne a wata unguwa mai suna Yaya Crescent Ajegunle Olodi Apapa. Ya kara da cewar lamarin ya afku ne a gidan daya daga cikin wadanda ake tuhumar da misalin karfe 11:50pm.
Mai shari'ar ya bayyana cewa kafin a kama matasan ranar 11 ga watan goma, an zarge su da yunkurin taba ma yarinyar gaba, da kuma kakkamata ba tare da amincewar ta ba.