Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Sama Mana Ayyukan Kwarai, ba Achaba ba- Inji Matasa


Matasan Najeriya sune kusan kashi saba’in na al’ummar kasar, amma yawancinsu ba su da ayyuka ko sana’o’in kirki. A lokacin zaben da aka yi a Najeriya cikin wannan shekarar ta 2015, matasan sun taka muhimmiyar rawa, duk da cewa a lokuta da yawa ‘yan siyasar sun yi amfani da su wajen bangar siyasa.

Yanzu haka dai matasan sun fara korafin cewa ‘yan siyasa sun watsar da su, ga dukan alamu sun manta da alkawulan da suka dauka lokacin da suke yakin neman zabe.

Malam Danladi Aboki Zaria, matashi ne da ya fadi cewa ‘yan siyasa ke tura matasa yin bangar siyasa. Amma abin duba wa shine, babu ‘yayansu ko daya dake yin wannan aika-aikar. Don kuwa suna makarantu, ba ma irin na gwamnati ba amma na kudi, abinda kuma har yanzu wasu matasan ba su gane ba.

Malam Danladi ya kara da cewa, yawancin lokuta sai ka ga ‘yan siyasa sun ba matasan da suka taya su yakin neman zabe kyautar babura don yin achaba, daga nan kuma sai ka ga matasan sun zarce zuwa daba. Ya kuma ce abin da ya fi dacewa shine a gina makarantu ko masana’antun da matasa za su sami aikin yi don achaba da bangar siyasa ba aiki ba ne.

“Duk dan takarar da ya fito takarar wani mukami a Najeriya, kamata yayi matasa su tambayeshi wane irin ayyuka zai kirkiro masu? A cewar Malam Danladi. Ya kuma ce akwai masana’antu da yawa a kasar yanzu amma kusan sun durkushe.

Ga karin bayani daga Babangida Jibrin.

XS
SM
MD
LG