Taimako nada matukar muhimanci a kowane irin hali mutun yasamu kan shi. Sau da yawa mutane basu taimaka ma mabukata, a wasu lokkuta masu hali basu taimakon ma marasa hali. Taimako bayana nufin kaba mutun wani abu ba. Dariya, gaisuwa, budema mutun kofa a wajen jama’a, da dai abubuwa makamantan hakan. Suma wasu abubuwa ne da mutane da dama sukan ji dadi kuma yakan nuna halin mutun.
Wata mata Anny Deese, tana da jaririya ‘yar wata hudu, a lokacin da take tafiya daga garin Boston zawa garin Philadelhpia, ta fuskanci matukar damuwa domin kuwa tana dauke da jakunkunan, da abubuwa da yawa a hannunta, hakan yasa bata iya yin wani abu awannan lokacin. Jama’a kuma nata kallonta babu wanda yabata wani taimako.
Ana cikin haka sai ga wata mata ta taimake ta, ta daukar mata kanyanta har suka isa inda zasu. Suna cikin jirgi sai ta lura da wannan matar ta zauna a wajen da aka ajiye ma masu kudi wato “First class” duk da haka bata san kowacece wannan matar ba. Bayan sun isa garin da zasu, sannan ta iya gane cewar ashe Chelsea Clinton ce, ‘yayar tsohon shugaban kasar Amurka, kana kuma mahaifiyar ta itake neman kujerer shugaban kasar Amurka. hakan yasa matar cikin tunani cewar ashe masu hali kan taimaka ma na kasa da su?