A Najeriya dai rayuka da dama ne ke salwanta ta sanadiyar tashe-tashen hankali dake da nasaba da fadan kabilanci ko addini, musamman a jihohin arewacin kasar.
Domin magance wannan matsalar nema yasa yanzu wata cibiyar wanzar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da kirista ta Interfaith Dialogue For Peace, IDFP, tare da hadin gwiwar cibiyar shiga tsakani ta King Abdul’aziz International Center for Interfaith, KAICIID, sun shirya tarukan kawo fahimtar juna a jihohin Filato da Taraba da Benue da Kaduna da kuma jihar Zamfara da ke fama da tashe tashen hankula.
Yayin wannan gangami na kawo fahimtar juna, tawagar cibiyar ta gudanar da taron ne a yankin Mambila, a garin Gembu inda aka tattaro masu ruwa da tsaki, to amma da farko sai da suka ziyarci mai martaba lamdo Mambilla Dakta Shehu Audu Baju, inda basaraken ya yaba da wannan kokari.
Jihar Taraba dai kaurin suna a tashe tashen hankula, batun da jami’ar cibiyar wanzar da zaman lafiyan a Taraban Liyah A. Solomon ke cewa dole a tashi tsaye, ta kuma nuna farin cikinta.
Domin Karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum