Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharudan ASUU Na Janye Yajin Aiki Sun Sa Dalibai Cikin Fargaba


Daliban Jami'ar Ibadan
Daliban Jami'ar Ibadan

Kungiayr ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne don mutunta umarnin kotun da’ar ma’aikata da na daukaka kara, ba wai don gwamnati ta biya mata dukkanin bukatunta ba tana mai cewa muddin gwamnati bata biya mata bukatunta ba akwai yiyuwar a koma gidan jiya.

Kungiyar ASUU dai ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne a wani taron shugabanninta da aka fara a daren jiya Alhamis wanda ya kai safiyar yau Juma’a, sannan suka cimma matsayar mutunta umarnin kotu na dakatar da yajin aikin, kafin su iya daukaka kara la’akari da shawarar da lauyoyin kungiyar suka bayar kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar a matakin kasa, Chris Piwuna ya shaida wa Muryar Amurka.

Matakin na kungiyar ASUU ya biyo bayan korafe-korafen ‘yan Najeriya, shiga tsakani don sulhu da shugaba Muhammadu Buhari da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila suka yi, in ji shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.

Duk da cewa sharadin da malaman suka bayar a yayin dakatar da yajin aikin ya sanya fargaba a zukatan dalibai, iyaye da ma wasu ‘yan Najeriya, wasu dalibai sun yi imanin cewa zasu sami damar kammala karatunsu da zarar malaman sun koma bakin aikinsu.

A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Abdulganiyu Rufai Yakubu, ya ce dukannin bangarorin biyu basu nuna kulawa da dalibai da iyayen da l’amarin ya shafa ba, yana mai cewa ya zamo wajibi ASUU da gwamnati su yi hakuri da wani abun da suke nema don a sami bakin zare kan wannan rikicin da yaki-ci-yaki cinyewa.

Idan ana iya tunawa dai kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin gargadin mako 4 ne a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022 da muke ciki, wanda ta kara tsawaitawa sakamakon yadda gwamnati ta gaza biya mata bukatunta kafin ya rikide zuwa yajin aikin sai baba ta gani a cikin watan Agusta.

A yayin da ake tsaka da yajin aikin ne gwamnatin tarayya ta yi rajistar wasu kungiyoyin malamai biyu na CONUA da NAMDA, sai dai ASUU ta ce hakan ya saba ka’ida kuma ba ta damu da matakin da gwamnati ta dauka ba.

Duk kokarin ji ta bakin ma’aikatar ilimi da ta kwadago wadanda ke kan gaba a tattaunawa da kungiyar ASUU don samo mafita kan lamarin dai ya ci tura a lokacin hada wannan rahoto.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00

XS
SM
MD
LG