Kwangilar buga lasisin tuki da aka ba wani kamfanin kasar waje ba tare da fayyacewa ‘yan kasa zahirin abubuwan da wannan yarjejeniyar ta kunsa ba, ita ce ta harzuka wadannan ma’aikata a wani lokaci da ayyukan harhada takardun ababen hawa da na buga lambobin motoci suka koma hannun wani kamfanin kasar waje, mafarin wannan yajin aikin kenan na tsawon kwanaki biyu, inji sakataren yada labaran kungiyar SYNPAT Oumarou Moussa.
Sai dai hukumomi na cewa babu kamshin gaskiya akan dukkan abubuwan da wadannan ma’aikatan ke korafi akansu.
Diallo Amadou ISSIFI, shine daraktan ofishin ministan sufurin, yace sun shafe wunin shekaranjiya Talata su na tattaunawa kuma sun sami fahimtar juna akan koke-koke 11 daga cikin 12 da ma’aikatan suka gabatar. Abinda ba su fahimci juna akansa ba shine batun takardun yarjejeniyar da suka bukaci a basu, kuma wannan doka ba ta yarda a baiwa kowa takardar yarjejeniyar ba har sai an wallafa ta a ma’ajiyar takardun hukuma da ake kira journal official da turanci. Yanzu haka ana cikin sake duba wannan yarjejeniya domin yi mata gyaran fuskar da za ta yi daidai da bukatun ‘yan kasa. Saboda haka rashin fahimtar dake tsakanin gwamnati da ma’aikatan ba ta kai inda za a jingine aiki ba amma ko gobe a shirye muke a sake bude tattaunawar, a cewar Diallo.
Wadannan jami’ai sun lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya har sai hakarsu ta cimma ruwa saboda haka kungiyarsu ta fara hangen shiga wani yajin aikin a makon gobe muddin basu ji wata amsa mai gamsarwa ba.
Facebook Forum