Kungiyar ‘yan jarida ta duniya dake aikin binciken wasu takardu da suka bayyana daga wani ofishin Lauyoyin da ke kasar Panama, sun bayyana matsayar da suka cimma ta gano cewa wasu abokan huldar shugaban Rasha Vladamir Putin sun shigar da kudin da ya kai Dalar Amurka Biliyan 2 zuwa boyayyun asusun bankunan kasar.
Wannan samamen fitar da kudin ya kwashe shekaru kusan 40 ana yinsa. Kungiyar bin diddikin mai suna International Consortium of Investigatijve Journalists a turance, ta hada kai ne da wata jaridar Jamus mai suna SITTOH- ZETA-SHUN (Sueddeusche Zeintung) tare da wasu kamfanonin jaridu sama da guda 100.
Sun bayyana cewa, wasu takardu sama da Miliyan 11 da Dubu Dari 5 ne suka bulla daga ma’aikatar shari’ar mai zaman kanta ta MOSSEK FONSEKA (Mossack Fonseca) da ke Panama, inda suka nuna hada-hadar wasu mutane da kamfanoni da dama dake da alaka da Shugaba Putin tun daga shekarar 1977 har zuwa shekarar 2015.
Haurawa da kudade zuwa boyayyun asusun ajiyar a kasashen ketare ba lallai ne ya zama bisa doka ba, domin ana iya haka don inganta kasuwancin kasashen duniya. To amma sau tari masu ruwa da tsaki a bude irin wannan asusu masana shari’a, basu cika bin diddigin gano ko kudin na halaliya ne ko kuma na almundahana.