Babar mai shari'ar tace kotu tayi damarar tunkarar kararrakin zabe da zara an gabatar dasu saboda hakkin tabbatar da an aikata gaskiya ba tare da nuna banbanci ba ya rataya ne a wuyan fannin shari'ar kasar kamar yadda kundun tsari ya tanada..
Bisa ga rantsuwar da suka yi zasu yi aikinsu tsakani da Allah. Tace sun himmatu da aikinsu. A matsayinsu na masu shiga tsakani zasu yi aikinsu da adalci domin kare muradu da manufofin dimokradiya.
Tace tana yiwuwa a samu rashin fahimta a lokacin zabe da bayan zabe. Idan hakan ya faru ba'a samu yadda ake so ba kotuna zasu magance duk irin wadannan matsalolin.
Alkaliyar Alkalan Ghanan tayi jawbinta ne a lokacin da take kaddamar da wasu takardu akan shigar da kararrakin zabe.
Su ma 'yan sandan kasar ta bakin DSP Imam Huseini sun shirya tsaf su tunkari kowace irin matsala ta taso lokacin zabe da bayan zaben.
Ga rahoton Baba Makeri da karin bayani.