Wani bincike da Cibiyar Nazarin Raya Akidojin Demokradiya ta Amurka ta CDD ta gudanar ya nuna cewa akasarin mutanen kasar Ghana duk sunyi imani da cewa Hukumar Zaben kasar zata iya gudanarda ingantaccen zabe na adalaci kuma cikin kwanciyar hankali a ran 7 ga watan Disamban nan mai zuwa, lokacinda za’a yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin kasar.
A hirar da yayi da Muryar Amurka Kojo Asante, wani babban kusar Cibiyar ta CDD, yace yanzu mutanen Ghana da dama suna dada samun karfin gwiwar amincewa da Hukumar zaben kasar tasu.
Sai dai kuma binciken na CDD ya nuna cewa akwai damuwa a yankin arewancin kasar din inda wasu ke jin tsoron barkewar tashin hankali bayan an kamalla kirga kujri’un da aka jefa a lokacin zaben.