An sayar da tikitin ne a wani shago da ake kira KC Mart, a garin Simpsonville, lambar dake jikin tikitin ta yi daidai da lambobi shida da aka samar ranar Talata, duk da cewa, yana da matukar wuya mutum ya iya samun lambobin duka daidai.
Wanda ya sami nasarar cin cacar dai zai zamanto Biloniya idan ya rika karbar kudinsa duk shekara na tsawon shekaru 30. Kuma wanda ya sami nasarar zai iya karbar zunzurutun kudi dala Miliyan 877 lokaci daya, wannan dai shine zabin da yawancin mutanen da suka ci ke karba.
Jami’an dake lura da harkokin cacar lotiri suna da masaniyar inda aka sayar da tikitin da ya ci cacar da kuma lokacin da aka sayar da tikitin, amma ba zasu san mutumin da ya sayi tikitin ba. A Jihar South Carolina duk mutumin da ya ci cacar lotiri zai iya kin bayyana kansa ga jama’a, bayan an kammala binciken tabbatar da cewa shine ya ci, a cewar shugaban gudanar da harkar cacar lotiri Tony Cooper.
Facebook Forum