Wani jami’in tsaro da bai yarda a bayyanar da sunansa ba a gundumar Baghlan, inda lamarin ya auku, ya fadawa Muryar Amurka cewa Dakarun kasar Afghanistan na rundunar ANA guda 31 da yan sanda tara suna cikin wadanda suka mutu.
Wani mai Magana da yawun kungiyar ‘yan tawayen yace a lokacin harin, sun kuma kame tungayen sojoji guda biyu, sannan kuma sun hallaka sojan Afghanistan 70, koda yake sau da yawa ‘yan Taliban din sukan yi karin gishiri a duk wani adadi da sukan bada.
Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan da Taliban ta kwace wani muhimmiyar tungar dakarun Afghanistan ta ANA a kusa da gundumar Faryab, suka kashe sojoji da dama kana suka kama wasu.
A hali da ake ciki kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedi a yau Laraba cewa fadan da aka kwashe kwanaki ana yi a kudu maso gabashin birnin Ghanzi, ya haddasa tsananin kunci rayuwa a kan fararen hula.
Facebook Forum