WASHINGTON, D.C —
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya yi kira ga Isra’illa da ta dakatar da yunkurinta na mamaye zirin gaza, wato yunkurin da masu adawa da hakan suka ce zai iya ruguza yiwuwar samun natsuwa a yankin.
Pompeo ya ziyarci Isra’illa a ranar Alhamis domin tattanauwa da Frai ministan Isra’illa Benjamin Netanyahu.
Lokacin da Pompeo ke zantawa da jaridar Israel Hayom ya umarci shugabannin Isra’illa da su yi tunanin duk abubuwan da zasu iya biyo baya, su kuma yi tunanin yadda za su magance irin matsalolin da ka iya tasowa, da kuma yadda za a gudanar da wannan shirin ba tare da barinsa ya shafi zaman lafiya ba.
Isra’illa tana son ta mamaye a kalla kashi 30 na yankin na zirin gaza.
Facebook Forum