Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Limami A Jihar Sakkwato Ya Jagorancin Magoya Bayansa Yin Sallar Idi


Wasu masu Salla a Masallaci
Wasu masu Salla a Masallaci

Duk da yake a hukumance ba a samu rahoton ganin watan Shawwal ba jiya Litinin 29 ga Ramadan a Najeriya, wani malamin Musulunci a Sakkwato Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya jagoranci mabiyan sa wajen yin Sallar Idin karamar sallah yau Talata.

SOKOTO, NIGERIA - Limamin dai ba wannan nan ne karo na farko ba da yake bijirewa umurnin Shugaban Majalisar koli kan lamurran addinin Musulunci a Najeriya, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar musamman kan batun da ya shafi ganin watan azumi Ramadan ko na Sallah.

A wannan shekara ma, Sheikh Lukuwa ya jagoranci magoya bayan sa wajen gudanar da Sallar ta Idi a Masallacin sa da ke shiyar Mabera da sanyin safiyar yau Talata.

Limamin ya kafa hujjar yin sallah da kuma ajiye azumi bisa ga samun rahotannin ganin wata a wasu wurare da ya hakikance da su a Jamhuriyar Nijar, duk da yake ya ce a Najeriya ma an samu wasu rahotanni na ganin watan Shawwal sai dai ba a tantance su ba.

Wannan Sallar dai ta sabawa umurnin Majalisar Koli kan lamurran Musulunci a Najeriya, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi wadda ta ayyana ranar Laraba 10 ga Aprilu a zaman ainihin ranar Sallar Idi, saboda ba a ga watan Shawwal ba ranar Litinin ta 29 ga Ramadan, saboda haka watan Ramadan zai cika kwana talatin ke nan.

Yanzu haka kusan dukkan Musulmi a Najeriya na dauke da azumi cikamakon na talatin kafin gobe Laraba su yi Sallar Idi.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Wani Malami A Jihar Sakkwaton Yau Ya Jagorancin Magoya Bayansa Yin Sallar Idi.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG