NIAMEY, NIGER - Yayin da al'ummar musulmi a fadin duniya suka gudanar da hawan idin babbar Sallar a yau Asabar 9 ga watan Yulin 2022, musulmi a jamhuriyar Nijar su ma sun yi sallar idin a sassan kasar, ciki har da birni N’konni inda mahukuntan yankin suka yi fatan samun zaman lafiya.
A babban birnin Yamai, shugaban kasa Bazum Mohamed ya halarci hawan idin babbar Sallar tare da Firai Minista Uhumudu Mahamadu, da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar, da ma sauran al'uma.
Mahukunta sun yi amfani da wannan damar domin yin kira ga al'umma akan yin addu'o'in samun zaman lafiya da damina mai albarka, kamar yadda Abdu Mahamidu magajin garin birni N'Konni ya bayyana jim kadan bayan kamalla hawan idin na babbar Salla.
Shi ko mai martaba sarkin birni N'Konni ya yi kira ga jama'a da su sake halayensu idan suna son Allah yayi musu jinkai, musamman a irin yanayin da a ka shiga na rashin ruwan sama a yankin kusan sati uku kenan.
Tun dai lokacin da aka gama Sallar, limamai suka yanka ragunan layya, abinda ke share fage ga kowane musulmi da yayi koyi da hakan don tunawa da ragon da Allah ya bai wa Annabi Ibrahima don kar ya yanka dansa Annabi Isma'ila.
Saurari rahoton Harouna Mamane Bako: