Corker yace wannan zaman yana daga cikin matakan da majalisa zata dauka na nazarin ikon da Amurka ke da shi, da kuma hanyoyin amfani da makaman nukiliya. Yace majalisa bata sake waiwayar wannan ba tun alif da dari tara da saba’in da shida, ya kuma ce lokaci ya yi da ya kamata a sake nazari a kai.
Muhawara kan wanda yake da ikon bada izinin amfani da makaman nukiliya ya taso ne a majalisa bayanda shugaba Donald Trump ya yi barazana a cikin watan Agusta cewa, Koriya ta arewa tana iya fuskantar martanin da duniya bata taba gani ba, idan ta cigaba da ayyukanta na nukiliya.
Corker, wanda ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa zabe ba a shekara ta dubu da biyu da goma sha takwas, ya yi sa’in-sa da shugaba Trump a bainar jama’a lokuta da dama a watan da ya gabata.
Facebook Forum