Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Zai Dauki Matakan Hana Kafofin Tsaron Cuba Mamaye Harkokin Tattalin Arziki


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A ci gaba da warware dangantaka tsakanin Amurka da Cuba shugaba Trump ya sanar da daukan matakan hana kafofin tsaron Cuba mamaye harkokin tattalin arziki tare da hana Amurkawa zuwa kasar ta Cuba ko yin kasuwanci da ita

Gwamnatin Shugaban Amurka Donald ta ba da sanarwar cewa za ta fara aiwatar da wasu canje-canjen da za su dauke harkokin tattalin arziki daga hannun rundunar sojin Cuba da hukumar leken asirin kasar da kuma sauran fannonin tsaro, sannan ta kuma kakaba takunkumin tafiye-tafiye da kasuwanci kan Amurkawan da ke harka da ‘yan Cuba.

Akasarin Amurkawan da ke shirin kai ziyara zuwa wannan tsibirar kasa, dole ne su yi hakan ta wajen bin tawaga da kamfanonin Amurka ke tafi da su. Dole ne kuma matafiyan su samu rakiyar wani wakilin kungiya ko hukumar da ta dauki dauyin tafiyar.

Trump ya fara sanar da manufofinsa kan Cuba ne ranar 16 ga watan Yuni lokacin da ya kai ziyara zuwa wata matattarar ‘yan kasar Cuba da ake kira ‘Little Havana, da ke Miami, to amma babban bankin Amurka zai tsame duk tafiye-tafiyen da aka tsara su gabanin bullo da wannan sabon tsarin.

Yau Alhamis ne sabon tsarin zai fara aiki, wanda zai zama wani dan koma baya ga maido da huldar diflomasiyyar da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya yi da Cuba a 2015, bayan sama da shekaru 50 da Amurka ta yi ta na haramta hulda da wannan kasa mai ra’ayin gurguzu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG