Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA sun kama wani dillalin miyagun kwayoyi da ke da zama a kasar Brazil.
An kama Okafor Okwudili Moses, wanda ya ajiye kilogiram 2.55 na hodar iblis da aka gano a bayan gidan sashin shigowa kasar fannin na’aura na filin saukan jiragen saman Murtala Muhammed a jihar Legas.
Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A cewar Babafemi, an gano hodar ibilis din ne a ban dakin filin tashi da saukan jiragen saman Murtala Muhammed a ranar Juma’a 12 ga watan Nuwamba bayan da wani mai fataucin miyagun kwayoyi ya jefar da shi.
Moses ya jefar da kwayoyin ne bayan da ya tsorata kan yiyuwar jami’an hukumar dake sashen gano miyagun kwayoyi da ke jibge a filin jiragen saman su kama shi.
A ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba ne ainihin mai kayan mai suna Okafor ya isa filin jiragen saman daga kasar Brazil ta kamfanin jirgin saman Ethiopia kuma jami’an NDLEA suka kama shi daga bisani.
A yayin da ake masa tambaya bayan kama shi da aka yi, Okafor ya tabbatar da cewa shi ne mamallakin haramtaccen miyagun kwayoyin da aka bankado kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.
A wasu ayukan hukumar NDLEA da ta gudanar a fadin kasar kuma, an gano sama da kilogiram dubu 6 da 043 da digo 857 na haramtattun miyagun kwayoyi a jihohi biyar da suka hada da Adamawa, Ondo, Ekiti, Edo da Ebonyi tare da lalata gonakin tabar wiwi sama da hekta biyu in ji Babafemi.
Babafemi ya kara da cewa hukumar ta kuma sami nasarar kama wani da ake zargin jami’in tsaro na bogi ne mai suna Abdullahi Mohammed, wanda ya yi ikirarin cewa yana aiki a daya daga cikin hukumomin tsaron kasar a garin Mubi na jihar Adamawa inda aka kama shi da rukuni hudu na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4 a kan hanyar Bazza zuwa Michika.
Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutane hudu da ake zargi a wurare daban-daban a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa, dauke da miyagun kwayoyi iri-iri kamar su tabar wiwi, Diazepam, Exol-5 da kuma kwayar Tramadol.
A jihar Ondo, NDLEA ta sami nasarar kama mutane uku da suka hada da Alabi Idowu, Oluwatomipe Olorundare da Finity Sunday a ranar Litinin 15 ga watan Nuwamba kuma an kwato jimillar tabar wiwi dubu 2 da 771 a hannunsu a sansanin Oke Ogun da ke garin Ipele na karamar hukumar Owo, yayin da aka kama wata Joy Peter mai shekaru 59 da tabar wiwi sama da Kilogram 39 da kwayar Tramadol a ranar Laraba 17 ga Nuwambar da mu ke ciki in ji, Babafemi.
Baya ga haka, hukumar ta kama sama da kilogram dubu 2 da 832 na miyagun kwayoyi tare da lalata gonakin wiwi sama da hekta biyu a wasu sassan jihar Ekiti, yayin da aka kwato kilogiram dubu 2 da 582 na tabar wiwi a ranar Talata 16 ga watan Nuwamba daga dajin Itapaji na garin Ipao a karamar hukumar Ikole, kuma ta kwace kilogiram 250 daga dajin Ise na karamar hukumar Ise-Orun inda aka lalata gonar tabar wiwi a ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba.
A jihar Ebonyi kuma,jami’an hukumar NDLE sun kama wani Ivoh Chukwuemeka mai shekaru 29 tare da budurwarsa Ogbonna Peace, mai shekaru 18, a kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki tare da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 20.357 a ranar Juma'a 19 ga watan Nuwamba.
An kuma kama wani Lucky Okhian da Aaron Monday da tabar wiwi kilogram 377.5 a karamar hukumar Owan ta yamma da kuma dajin Okpokhumi a karamar hukumar Owan ta Gabas ta jihar Edo.
Da yake jawabi a game da kama mai fataucin miyagun kwayoyi Okafor da sauran wadanda ake zargi da kuma miyagun kwayoyin da aka kwace daga jihohin, Shugaban Hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa, Mai Ritaya ya yabawa jami’ansa da su ke gudanar da ayyuka a fadin ofisoshin hukumar bisa yadda suka daura damarar yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a kasar nan.
Buba Marwa ya ce hukumar na tabbatar da cewa ta na daukan matakan da suka dace kan miyagun mutanen don kawo karshen matsalolin da suka shafi fatauci da tu’amalli da miyagun kwayoyi a kasar.