Yayin da makonni biyar suka rage a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar da ke yankin arewacin Najeriya, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ta ce, binciken ta ya nuna wasu daga cikin ‘yan takara a zaben na mu’amala da ababen sanya maye.
Fiye da mako guda kenan Jam’iyyar APC mai Mulki a jihar ta Kano ta mika sunayen ‘yan takarar shugabancin karamar hukuma da mataimakansu da kuma masu neman kujerar kansiloli a kananan hukumomin jihar ta Kano 44.
Ya zuwa yanzu dai hukumar ta NDLEA da ke yaki da ababen sanya maye a Najeriya ta ce tayi aikin gwajin jini ga ‘yan takara fiye da 250 wadanda ke neman kujerun shugaban karamar hukuma, mataimaki da kuma kansiloli a 19 daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar ta Kano.
Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari sun fara tsokaci game da wannan aikin gwaji.
Comrade Abdulrazak Alkali kenan, guda cikin kungiyoyin fararen hula a Najeriya.
Sai dai hukumar ta NDLEA dake gudanar da wannan aikin bincike akan ‘yan takara, ta ce ya zuwa yanzu rahotan aikin nata ya nuna wasu daga cikin ‘yan takarar na mu’amala da ababen sanya maye, amma lokacin zata kwarmata sunayen da kananan hukumomin da suka fito bai yi ba.
To amma sanata Masa’udu El-Jibril Doguwa guda cikin dattawa a Jam’iyyar APC a jihar Kano na cewa.
Abin jira a gani dai shi ne, ko Jam’iyyun da aka gano ‘yan takarar su na mu’amala da miyagun kwayoyi zasu sauya su da wasu ko kuma zasu kau da kai.