‘Yan bindigar dai sun yi garkuwa da farar fatan ne tare da direbansa, a lokacin da suke wani aiki a kauyen Yakila dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Tuni dai gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa domin nuna ta’aziyyarta ga gwamnatin kasar Lebanon. Da take yi wa sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani, sakatariyar yada labaran gwamnan jihar Neja, Madam Mery Barje, ta nuna rashin jin dadin gwamnatin ga faruwar wannan al’amari.
Yau Alhamis ake sa ran rundunar ‘yan sandan jihar Neja, za ta yi karin haske kan wannan lamari da ya faru, tare da cikakken bayanin abin da ya faru.
Sai dai masu sharshi na ganin irin wannan al’amari zai iya shafar dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen biyu, amma tsohon jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu, Ahmad Musa Ibeto na ganin ba haka abin yake ba, domin hakan na faruwa a kasashen duniya.
A kalla sojojin Najeriya uku da ‘dan bindiga guda ne suka mutu, a lokacin wani artabu da aka yi tsakanin jami’an tsaron da ‘yan bindigar lokacin da aka sace wannan farar fata ‘dan kasar Lebanon.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum