Wani ma’aikacin lafiya dan kasar Amurka da a bayyana jinsinsa ba, ya kamu da cutar Ebola a lokacin da ya ke aiki a kasar Saliyo, inda yanzu haka aka kwantar da shi a wani asibiti da ke Jihar Maryland.
Hukumomi sun ce mara lafiyan, wanda ya je kasar ta Saliyo domin tallafawa marasa lafiya, ya isa wata cibiyar kula da lafiya ne a yau juma’a bayan da aka kawo shi a wani jirgi a kadaice.
Likitocin da su ka duba mara lafiyan sun ce yana cikin wani mawuyacin hali.
Sai dai ya zuwa yanzu, cibiyar kiwon lafiyar ba ta fitar da wani karin bayani game da ko wanene mutumin ba, wanda ya kasance shi ne Ba’amurke na 11 da ake yiwa maganin cutar ta Ebola a Amurkan.
Da farko an maida wata mace soja ‘yar Burtaniya zuwa gida tare da wasu mutane biyu da ta yi mu’amulla da su, bayan da ta kamu da cutar a lokacin da ita ma ta ke aikin jin-kai a kasar ta Saliyo.
A ranar alhamis din da ta gabata Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce cutar ta Ebola ta hallaka sama da mutane 10,000, yawancinsu a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Saliyo wadanda duk a yammacin Afrika su ke.