Babban kwamishinan hukumar kula da 'yancin Bil'Adama,naMajalisar Dinkin Duniya ko MDD, Zeid Ra'ad Al-Hussein, yayi kira ga Turkiyya ta kyale a gudanar da bincike mai zaman kansa, kan jerin rahotanni masu tsoratarwa, cewa ana keta hakkin Bil'Adama a kudu maso gabashin kasar inda ake fama da rikici.
Kiran da MDD tayi jiya talata na neman ganin an gudanar da bincike bil-hakki da gaskiya, yana zuwa ne a dai dai lokacinda shugabanni a turai suke son gwamnatinTurkiyyar, ta hana korarar bakin haure da 'yan gudun hijira zuwa Turai, a gefe daya kuma, tana matsawa gwamnatin lamba tayi garambawul ga dokokin kasar kan yaki da ta'addanci, wadanda masu adawa suka ce ana amfani da su wajen muzgunawa masu sukar lamirin gwamnatin.
Wata sanarwa da MDD ta bayar, tace kwamishin Zeid, ya sami rahotanni cewa, 'yan sari ka noke,ko kwararrun maharba da binidga da gangan suna kashe farar hula ciki harda mata da yara, haka nan ana amfani da tankunan yaki na sojoji da wasu kayan yaki wajen kashe ire-iren wadannan mutane.