Fashewar bam din ya faru ne misalin karfe 11.30 na safiyar yau a dakin adana bamabamai na ofishin 'yansanda dake Jimeta.
Alkalumma da rundunar 'yansandan jihar ta fitar sun nuna jami'an 'yansanda hudu ne suka yi hasarar ransu cikinsu har da mataimakin babban jami'in kwance bamabamai da nakiyoyi. Wasu kuma da dama sun samu raunuka.
Da yawa cikin wadanda suka jikata mata ne masu aikin ba motoci hannu d ake sani da suna yellow fever.
Kwamishanan 'yansandan jihar Malam Muhammad Gazali a harabar ofishin da bam din ya tashi ya shaidawa Muryar Amurka cewa lamarin 'yansanda ne kawai ya shafa bai shafi fararen hula ba domin yaji wai an ce akwai yaran makaranta da lamarinn ya rutsa dasu. Yace babu abun da ya samu yaran makaranta. Babu makaranta kusa da ofishin 'yansandan.
Kwamishanan ya tabbatar cewa ba hari aka kawowa 'yansandan ba. Nakiya da aka kwato daga 'yan Boko Haram ce ta fashe. Hr yanzu akwai sauran nakiyoyin da basu fashe ba saboda haka suna kafa kafa.
Shi ma mataimakin gwamnan Adamawa Injiniya Martin Babale wanda ya kai ziyarar gani da ido inda yace ganin ofishin yana cikin gari da gine gine kewaye dashi ba karamar illa fashewar bam din ya jawo ba. Yace gwamnati zata dubi yiwuwar sakewa ofishin matsuguni saboda kaucewa sake aukuwar lamarin..
Ga karin bayani