Taron da Fulanin suka gudanar a garin Pandogari domin shawo kan matsalar da ta addabi jihar, ya samu halartar fulanin da yawa tare da jami'an gwamnati da na tsaro.
A wurin taron ne rundunar sojin Najeriya ta gargadi 'yan bindigan su mikawa hukuma bindigoginsu cikin mako guda ko su hadu da fushin hukumar. Kwamandan rundunar sojojin ta daya dake Kaduna Manjo Janar Adeniyi Oyebade yace kisan jama'a da fyade da ake yiwa mata da satar shanu sun isa haka.
Inji kwamandan basu halarci taron domin su roki kowa ba. Idan masu aikata laifin basu daina cikin ruwan sanyi ba to zasu daina alatilas, da karfi da yaji.
Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa Alhaji Huseni Boso yayi karin haske akan dalilin da suka shirya taron. Yace tunda aka nuna cewa wasu Fulani makiyaya ne suke aikata ta'asar kuma an sansu ya sa suka gayyacesu su zo taron domin fadawa juna gaskiya.
A wurin taron an samu 'yan bindiga uku da suka bayyana suka kuma mika kansu. Daya daga cikinsu mai suna Malam Shuri yace shi bai taba zuwa barna a Neja ba amma yayi a Kaduna saboda abun da aka yi masa. Yace sun san wadanda suke kai hari Neja. Yace yaransu ne da suka taso daga Zamfara da Katsina su ne suka aikata hare-haren kwana kwanan nan.
Shugaban karamar hukumar Rafi Gambo Tanko Kagara yace fatansu shi ne a samu masalaha akan al'amarin domin akwai garuruwa 15 da babu kowa ciki sakamakon hare-haren da aka kai masu.
Shi ma mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Getso yace idan fulanin ba zasu zauna lafiya ba to su bar jihar gaba daya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.