Darektan Sashen Afirka na Muryar Amurka, Negussie Mengesha, da wasu manyan VOA sun taya VOA Hausa murnar cimma mizanin kaiwa ga masoya miliyan daya a shafin Facebook.
VOA Hausa Ta Yi Wata 'Yar Karamar Liyafa
 
1
Hagu zuwa dama: Leo Keyen, shugaban VOA Hausa; Ibrahim Alfa Ahmed, manajin edita mai kula da Intanet da kafofin sada zumunci; Negussie Mengesha, shugaban sashen Afirka na VOA.. Fabrairu 13, 2017
 
2
Hagu zuwa dama: Steven Ferri, manajin edita mai kula da intanet da shafukan sada zumunci na Sashen Afirka; Leo Keyen shugaban VOA Hausa; Ibrahim Alfa Ahmed, manajin edita mai kula da Intanet da shafukan sada zumunci na Sashen Hausa; Negussie Mengesha, shugaban sashen Afirka na VOA; Solomon Chollom Jack, Babban Fardusa na TV na sashen Hausa. Fabrairu 13, 2017
 
3
Shugaban sashen Afirka, Negussie Mengesha, yana tattaunawa da shugaban sashen binciken labarai na Dakin Labarai na VOA, Tom Detzel, wanda ya halarci liyafar. Shugaban Sashen Hausa, Leo Keyen a dama yana kallo.
 
4
Julie Gresham ita ma tana diban abinci a lokacin wannan liyafa  Fabrairu 13, 2017
 
 
 
 
 
 
 
 
