A jiya Talata ne bayan da shugaban kasar Rasha Puttin ya gana da takwaransa na Turkiyya Tayyip Erdogan a birnin Saint Petersburg na Rasha, yace “a kokarin dawo da mu’amula ta hanyar cinikayya da tattalin arziki, yanzu haka an fara ta, amma zai ‘dauki lokaci.”
Erdogan yace kasashen biyu zasu dawo da yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakaninsu da ta kai Dala Biliyan 100, kuma za a gaggauta dawo wa da ita.
Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa, a shirye yake ya gina bututun iskar gas da kasar Rasha, kuma zai tattauna da Rasha don ganin Turkiyya ta gina wajen sarrafa makamashin Nukiliya na farko a kasar.
Kasashen biyu dai sun amince da sake wani zama domin samun hanyar da za a kawo karshen yakin da ake A Siriya. Baki daya kasashen biyu na goyon bangare daban daban a yakin basasar Siriya.