Kimanin mutane miliyan biyu ke rayuwa a wurin da babu ruwa da wutar lantarki inji MDD a yau Talata. A yayinda yan tawayen Syria ke kusawa cikin birnin Aleppo inda gwamnati ke da rinjaye, jami’an kiwon lafiya sun shaidawa tawagar MDD irin tsaka mai wuya da wannan birni mafi girma a Syria ke ciki
Dr. Zaher Shaloul na kungiyar likitocin Syria dake jihar Chicago a nan Amurka ya shaidawa jami’an MDD cewa kananan yara basu samun madara. Likitocin na fama da tsananin karancin magunguna, da rashin jini ga mabukata da sauransu, sa’annan babu abinci kuma babu iskar gas ta dafuwa..
Dr. Samer Attar da shi kuma ke aiki da kungiyar likitocin Syria a Chicago, ya nunawa jami’an hotunan kananan yara da aka yanke kafafunsu da kuma masu raunin kwakwalwa. Yace asibitin Aleppo tamkar yana cikin rami ne saboda an katangeshi da buhunan yashi don kareshi daga harin bama bamai. Yace a wani asibitin da yake aiki ana jinyar marasa lafiya ne a dakunan karkashin ginin, saboda gujewa hari a dakunan dake sama.