Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadiyar Amurka a MDD Ta Kai Ziyara Kasar Ghana


Wakiliyar Amurka Linda Thomas-Greenfield lokacin da ta kai ziyara kasar Ghana
Wakiliyar Amurka Linda Thomas-Greenfield lokacin da ta kai ziyara kasar Ghana

Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Linda Thomas-Greenfield ta yi kira ga Rasha da ta daina dora wa wasu alhakin hare-haren ba gaira ba dalili da ta ke kaiwa kasar Ukraine.

Jakadiya Linda ta bukaci Rasha da ta dakatar da yakin tsakaninta da Ukraine, ta kuma fara bayar da gudummawar samar da abinci a duniya.

Jakada Greenfield ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai ziyara a Arewa maso gabashin kasar Ghana, a wani bangare na ziyarar rangadin da ta ke yi a kasashen Ghana da Uganda.

Linda Thomas-Greenfield
Linda Thomas-Greenfield

Ziyarar Thomas-Greenfield dai ta kasance don tattaunawa kan yadda rikici tsakanin Rasaha da Ukraine ya kawo matsalar abinci a duniya. Da kuma ganawa da wasu manoma domin sauraron kalubalen da suke fuskanta.

Samun jari babbar matsala ce a fadar ta, don haka ne hukumar ta USAID ta sanar da bayar da kudade masu yawa don tallafa wa manoma, ta hanyar taimaka musu wajen magance kalubalen da su ke fuskanta. Dole ne mu shawo kan rikicin, kuma hanya daya tilo da za a iya shawo kan matasalar ita ce hada kai da aiki tare, a fadar ta.

A cewar Thomas-Greenfield, Ghana na da albarkatun da take bukata domin inganta samar da abinci.

Linda Thomas-Greenfield
Linda Thomas-Greenfield

Ta kuma tattauna da mata yan kasuwa da manoma domin sauraron kalubalen da suke fuskanta. Inda suka bayyana irin horo da suka samu wajen samun sabbin dabaru domin bunkasa harkokinsu.

Jakada Thomas-Greenfield ta ce gwamnatin Amurka ta na taimakawa manoma da dala miliyan 2.5 ta hanyar USAID a duniya.

Domin Karin bayani saurari rahotan Hawa AbdulKarim.

Jakadiyar Amurka a MDD Ta Kai Ziyara Kasar Ghana – 3’58”
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG