Jiragen yakin Turkiyya sun fafari karfafen jiragen yakin Rasha sumfurin jet daga kasarsu, daura da kan iyakar kasar Siriya, bayan aukuwar al'amarin a ranakun 3 da 4 na watan Oktoba.
A makon jiya Rasha ta fara kai hare-haren jiragen yaki kan wasu wurare a Siriya, inda ta ce ta na kai hare-haren ne kan wuraren ISIS da wadanda ta kira 'yan ta'adda, wato 'yan tawayen da ke adawa da gwamnatin Siriya.
Sakatare-Janar na NATO Jens Stoltenberg ya fadi yau Litini cewa ya gana da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Feridun Sinirlioglu don tattaunawa kan take-taken Rasha a Siriya.
Kwamitin gudanarwar kungiyar, ya ce hukumomin Turkiyya sun sha gargadi ga jiragen Rasha su fice daga sararin samaniyar kasar. Ya bayyana kutsen da abin da bai dace ba, sannan ya bukaci Rasha ta yi bayani.
Kafar Labaran Interfax ta Rasha ta ruwaito Ofishin Jakadancin Rasha a Turkiyya na tabbatar da faruwar al'amarin, sai dai har yanzu Rasha ba ta yi wani bayani kan al'amarin ba a hukumance.