Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Na Goyon Bayan Lebanon Yayin Da Ake Takun Saka Tsakaninta Da Isra'ila - Erdogan


Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, Turkiyya na tsaye tsayin-daka da kasar Labanon a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakaninta da Isra'ila, ya kuma yi kira ga kasashen yankin da su marawa Beirut baya.

Rikicin kan iyaka tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon na kara ta'azzara a 'yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar yakin Isra'ila da Hizbullah. Harin da aka kai a kan iyakar arewacin Isra'ila ya kai ga kwashe dubban mutane daga yankunan biyu.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

A jawabin da Erdogan ya yi wa 'yan majalisar dokoki na jam'iyyarsa ta AKP a majalisar dokokin kasar ya ce Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu na shirin gudanar da yakin Gaza zuwa yankin.

"Da alama a yanzu Isra'ila ta mayar da idanunta kan Lebanon bayan da ta lalata da kuma kona Gaza, muna ganin kasashen yammacin duniya suna baiwa Isra'ila goyon baya a sakaye," in ji Erdogan.

Gaza bayan wani hari daga Isra'ila
Gaza bayan wani hari daga Isra'ila

Ya ce shirin Netanyahu na kawo yakin Gaza zuwa yankin zai haifar da wani babban bala'i, yana mai cewa goyon bayan da kasashen yamma ke baiwa Isra'ila abin takaici ne.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG