Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Zata Kara Haraji Kan Kayan Dake Shiga Kasarta Daga Amurka


Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan .
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan .

A wani matsayi na mayar da martani Turkiya ta sanar da kara haraji akan kayan dake shiga kasarta daga Amurka

Kasar Turkiyya ta ce za ta maka harajin kan kayakin da ke shigowa daga Amurka na dalar Amurka biliyan 1.8, a matsayin maida martanin harajin da Shugaba Donald Trump ya saka kan karafa da dalmar da ke shigowa Amurka.

Kungiyar Cinakayyar Duniya ta WTO ta ce harajin da kasar ta Turkiyya za ta saka zai kai dalar Amurka miliyan 266.5 kuma kayan da harajin zai shafa sun hada da motoci da gawayin kwal, da fafar rubutu da shinkafa da kuma sigari.

Ministan Tattalin Arzikin Kasar Nihat Zeybekci ya fada a wata takardar bayani cewa kasar Turkiyya ba za ta yadda a dora ma ta, abin da ya kira "laifin matsalar tattalin arzikin Amurka ba."

Ya kara da cewa, "Mu na taka rawa ne wajen warware matsalar, ba wajen haddasa ta ba."

Ranar Laraba, kungiyar Tarayyar Turai ta bayar da sanarwar cewa ta kirga kayayyakin da Amurka ke sayarwa, wadanda za ta shiga saka harajin kashi 25% a kansu, matakin da kila zai kai ga ruruta yaki a fagen cinakayya muddun Shugaba Trump ya aiwatar da barazanarsa ta saka haraji kan motocin kasashen Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG